Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Cutar Kwalara Na Bazuwa A Jihar Ogun

Annoba: Cutar Kwalara Na Bazuwa A Jihar Ogun

104
0
Yayin da cutar kwalara ke bazuwa a Najeriya musamman arewacin ƙasar, rahotanni na cewa cutar tana yaduwa cikin sauri zuwa wasu sassan kasar, musamman kudu maso yamma.

Yayin da cutar kwalara ke bazuwa a Najeriya musamman arewacin ƙasar, rahotanni na cewa cutar tana yaduwa cikin sauri zuwa wasu sassan kasar, musamman kudu maso yamma.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Ogun da ke kudancin Najeriyar ta fitar da wata sanarwa ta hannun kwamishinar lafiya, Dakta Tomi Coker inda ta tabbatar da barkewar cutar a jihar.

Ta ce cutar ta fi ƙamari a tsakanin `yan okada masu ɗaukar fasinjoji da baburan haya da kuma `yan ina-da-bola da ke a yankin Magboro.

Ɗaya daga cikin wuraren da cutar ta fi ƙamari a jihar shi ne unguwar ta Magboro kuma rahotanni na nuna cewa ta fi bazuwa a tsakanin al’ummar arewa da ke zaune a yankin inda wasu ke alaƙanta bazuwarta da tafiye-tafiye a tsakanin fasinjoji daga arewaci zuwa yankin kudu maso yammacin ƙasar.

Wasu daga cikin iyalan da ƴan uwansu suka kamu da cutar sun bayyana cewa ƴan uwan nasu sun haɗu da ajalinsu sakamakon amai da gudawar.