Home Labaru Masha-Allah: An Sako Dalibai Da Malaman Da Aka Yi Garkuwa Da Su...

Masha-Allah: An Sako Dalibai Da Malaman Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

305
0
Samuel Aruwan, Mai Magana Da Yawun Gwamnatin Jihar Kaduna

Masu garkuwa da mutane da su ka sace dalibai da malaman makarantar Engravers College a Kaduna sun sakosu, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana.

Gwamnatin jihar Kadunan ta roki jama’a su kiyaye wajen ruwaito labarin tare da mutunta sirrin wadanda aka sacen, su kuma rungumi wadanda aka sacen da hannu biyu.

Ta ce kyamar su ko kawo bambancin kabila ko addini ba abu ne mai kyau ba.

A karshe ya ce gwamnatin jihar Kaduna za ta maida hankali wajen ganin natsuwar su ta dawo jikin su kamar da.