Home Labaru Korafi: Ya Kamata Buhari Ya Nada Mata Da Dama A Ministoci-Omowumi Ogunlola

Korafi: Ya Kamata Buhari Ya Nada Mata Da Dama A Ministoci-Omowumi Ogunlola

186
0

Majalisar wakilai ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari,  da ya yi karin mata a wajen nadin mukaman siyasa domin dinke barakar karancin mata da aka samu a majalisar dokokin ta kasa da kuma wajen nadin ministoci.

Wannan kiran ya biyo bayan wani korafi da wata ‘yar majalisa daga jihar  Ogun na jam’iyyar APC  Omowumi Ogunlola ta gabatar, wanda ta ce an gano karancin mata masu rike da mukaman siyasa a Najeriya, sannan kuma ana iya gyara ne idan Buhari ya nada karin mata a matsayin shugabannin ma’aikatu.

Majalisar Wakilai

Yar majalisar ta ce mata sun kasance abokan aiki a fannin siyasa da ci gaban al’adun kowace kasa, saboda haka Najeriya ba zata iya ware kanta ba.

Ogunlola ta ce daga cikin ‘yan majalisar dokoki 469, 19 ne kawai mata, inda 12 daga cikinsu ke majalisar wakilai,  ya yinda 7 ke a majalisar dattawa, wanda hakan ke nuna kaso 4 ne kawai cikin 100, sannan kuma hakan ya saba sosai da koyarwar kasashen duniya.