Home Home Tasgaro: CITAD Ta Ce Ana Sace Dukiyar Cin Hancin Da Gwamnati Ta...

Tasgaro: CITAD Ta Ce Ana Sace Dukiyar Cin Hancin Da Gwamnati Ta Kwato

86
0
ALIYU ZAKARI
Shugaban Cibiyar bunkasa fasaha ta CITAD Dr. Yunusa Zakari Ya’u, ya yi zargin cewar ikrarin yaki da cin hanci da rashawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi na samun tasgaro saboda yadda ake sace dukiyar da aka kwato

Shugaban Cibiyar bunkasa fasaha ta CITAD Dr. Yunusa Zakari Ya’u, ya yi zargin cewar ikrarin yaki da cin hanci da rashawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi na samun tasgaro saboda yadda ake sace dukiyar da aka kwato.

Ya’u yace duk da makudan kudaden da gwamnatin tayi nasarar kwatowa, shirin na fama da matsalar siyasa, yayin da kuma ake ci gaba da sace dukiyar da aka kwato daga barayin gwamnati.

Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito shugaban Cibiyar CITAD na jawabi wajen wani taro a Kano inda yake cewa, daya daga cikin matsalolin da gwamnatin Buhari ke fuskanta wajen yakin shine siyasantar da yakin da kuma sanya wasu mutane a gaba, yayin da shi kadai ne ke bayyana abinda ake kira cin hanci da kuma masu aikata laifin.

Ya’u yace yanzu haka akasarin ‘yan Najeriya na kallon an yafe wa mutanen da ake zargi da rub-da-ciki da kudaden talakawa da suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

Shugaban Cibiyar ya kuma bayyana cewar shirin baiwa ‘yan kasa damar tona asirin wadanda suka saci kudin jama’a domin karbar wani kaso na dukiyar da aka kwato baya aiki, saboda rashin kare lafiyar masu tseguntawa gwamnati ko kuma wadanda ake zargi na basu makudan kudade da suka fi na gwamnati domin rufa musu asiri.

Yunusa Zakari Ya’u, ya zargi ‘yan majalisu da kungiyoyin fararen hula da kuma kafofin yada labarai da gazawa wajen taka rawar da ta dace wajen yaki da cin hancin a Najeriya.