Home Labaru Difilomasiyya: Gwamnatin Nijeriya Ta Musanta Yunkurin Rufe Ofisoshin Jakadancin Ta

Difilomasiyya: Gwamnatin Nijeriya Ta Musanta Yunkurin Rufe Ofisoshin Jakadancin Ta

448
0

Gwamnatin Nijeriya ta musanta rahotonnin da ke cewa za ta rufe wasu ofisoshin jakadancin ta 80 daga cikin 110 da ta ke da su a kasashen duniya.

A jiya ne dai aka tashi da rahotonnin cewa kasar na yunkurin rufe 80 daga cikin ofisoshin jakadancinta fadin duniya.

Rahotannin dai sun ruwaito cewa, Nijeriya za ta rufe ofisoshin  ne saboda ba ta da halin ci-gaba da gudanar da su, sannan a kasafin kudin baya-bayan nan an ware kudin da za a gudanar da ayyukan ofisoshi talatin ne kadai.

Sai dai wani jami’an gwamnatin tarayya ya ce rahoton ba ya da tushe balle makama.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne, kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa, ya ce ofisohin jakadancin Nijeriya a fadin duniya su na cikin mummunan yanayi, inda kwamitin ya zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da su.