Home Labaru Siyasar Kano: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Muhammad Santsi Na Jam’iyyar APC

Siyasar Kano: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Muhammad Santsi Na Jam’iyyar APC

606
0

Kotun daukaka kara, ta tabbatar da nasarar cin zabe ga dan takarar kujerar majalisar wakilai na kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa Honarabul Mahmoud Muhammad Santsi.

Yayin yanke hukuncin, kotun ta tabbatar da Mahmoud Muhammad Santsi a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa a jihar Kano.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan samun shahadar cin zabe, Santsi ya bada shaidar yadda tun farko ya lashe zaben fidda gwani da tazara mai yawa, amma aka sauya sunan sa bayan sakamakon zaben ya isa Abuja. Bayan gamsuwa da hujjojin da ta samu, kotun ta tabbatar da nasarar Muhammad Santsi, inda ta umurci hukumar zabe ta kasa ta mallaka masa shahadar cin zabe da gaugawa.