Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar kungiyar lafiya ta duniya, sun kafa kwamiti domin yin kididdigar adadin yawan mata da kananan yaran da ke mutuwa a Nijeriya.
Ministan lafiya Isaac Adewole, ya ce gwamnati ta yi haka ne domin shawo kan matsalar yawan mace-macen kananan yara da mata da ake fama da shi a Nijeriya.
Bincike ya nuna cewa, mata 145 masu shekaru 15 zuwa 45 ne su ke mutuwa a dalilin matsalolin haihuwa, sannan a duk rana yara 2,300 ‘yan kasa da shekaru biyar ke mutuwa sanadiyyar kamuwa da cututtukan da za a iya kawar wa.
Shugaban cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko na kasa Faisal Shu’aibu, ya ce gwamnatin tarayya ta amince ta bude fannin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara a Nijriya.
Ya ce cibiyar su za ta hada hannu da cibiyar kawar da cutar shan-inna ta kasa domin samun kudaden da za a bukata wajen ganin an samu nasara.