Home Labaru Wata Sabuwa: Satar Mutane Ce Sabuwar Sana’ar Matasan Nijeriya – Buhari

Wata Sabuwa: Satar Mutane Ce Sabuwar Sana’ar Matasan Nijeriya – Buhari

318
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana garkuwa da mutane a matsayin sabon aikin yi ga matasan Nijeriya.

Buhari ya ce dawo da noman auduga da masaku zai taimaka wajen samar da aikin yi a Nijeriya, ya na mai bayyana rashin jin dadin shi game da rashin tsaro a kasar nan.

Yayin da ya ke raba irin auduga ga manoma dubu dari da za su yi noma a wannan shekarar a jihar Katsina, shugaba Buhari ya ce matsalar tsaro a Nijeriya na da alaka da rashin aikin yi ga matasa.

Shugaba Buhari, wanda ministan noma Audu Ogbeh ya wakilta, ya ce dawo da masana’antu da sana’ar saka a Nijeriya zai taimaka sosai wajen sama wa matasa aikin yi.

Ya ce kuskuren da su ka aikata a baya ne ya ke dawowa a wannan lokacin, ga matasa su na gama karatu amma babu aikin yi.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, matasan Nijeriya sun koma sana’ar satar mutane, da satar shanu da sauran ayyukan ta’addanci, kuma hakan ya na sanya tsoro a zukatan ‘yan Nijeriya.