Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya biya naira miliyan 30 a matsayin kudin sadakin zawarawa dubu 1 da 500 da su ka fito daga kananan hukumomi 44 da gwamnatin jihar ta aurar da su.
Da ya ke sanar da hakan a cikin jawabin da sakataren sa na yada labarai Abba Anwar ya sanya wa hannu, Ganduje ya ce za a yi amfani da wani bangare na kudin da gwamnatin ta bada domin saya wa sabbin amaren kayan daki da su ka hada da katifa, da gado, da madubi da sauran su.
Gwamnatin jihar Kano, ta ce ta ware Naira dubu 200 a matsayin kudin sadaki ga kowace amarya daga cikin zawarawa dubu 1 da 500.
Ya ce ba kudin sadaki kawai gwamnati ta biya wa amaren ba, a cikin ayyukan alheri da ta saba yi za ta saya wa kowace amarya kayan daki. Anwar ya kara da cewa, gwamnatin ta yi hakan ne domin saukaka wa ma’auratan wahalhalu da kashe kudi da sabon aure ke zuwa da su.
You must log in to post a comment.