Home Labaru Kisan ‘Yan Makaranta: Jami’an Tsaro A Kamaru Sun Kama Wani Matashi Da...

Kisan ‘Yan Makaranta: Jami’an Tsaro A Kamaru Sun Kama Wani Matashi Da Ake Zargi

279
0

Jami’an tsaro a Kamaru sun kama wani matashi da ake zargi da
kisan yara bakwai ‘yan makarantar Mother Francisca
International Bilingual Academy da ke Kumba a Kudu Maso
Yammacin kasar.

An kama matashin mai shekara 24, Ngwa Neba, wanda ake yi
wa lakabi da Kwamanda Zabbra ranar Talata ne a yayin da ya yi
yunkurin yi wa wani tsoho fashin CFA dubu 5.

Mutumin dai ya yi ihun da ya ja hankalin ‘yan sanda lamarin da
ya kai ga kama matashin, ‘yan sandan sun ci karfin sa inda kuma
ya ce shi dan a-ware ne.

Babban jami’in ‘yan sandan Meme, Chamberlain Ntou’ou Ndong
ya ce ya yi amanna mutumin yana cikin wadanda suka kashe
dalibai ‘yan makaranta bakwai ranar 24 ga watan Oktoba.

Ya ce jami’an tsaro ba za su gajiya ba sai an kama dukkan
mutanen da ke da hannu a kisan yaran.

Leave a Reply