Home Labaru Kisan Soleimani: ‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Birnin Abuja

Kisan Soleimani: ‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Birnin Abuja

383
0
Kisan Soleimani: ‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Birnin Abuja
Kisan Soleimani: ‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Birnin Abuja

Mabiya akidar Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja, sakamakon kisan da Amurka ta yi wa Kwamandan Sojojin Iran Janar Qassem Soleimani.

Masu zanga-zangar, sun kuma bukaci a saki jagoran su Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa Zeenat da ke ci-gaba da kasancewa a tsare.

Wata majiya ta ce, masu zanga-zangar da ke dauke da alluna, sun kuma kona tutar kasar Amurka tare da la’antar ta.

Daya daga cikin masu tattakin Saminu Azare ya shaida wa manema labarai cewa, sun wuce ta gaban jami’an ‘yan sanda, amma jami’an ba su ce masu uffam ba ballantana su dakatar da su.

Mai magana da yawun Shi’a a Nijeriya Ibrahim Musa, ya ce, sun gudanar da makamanciyar zanga-zangar a harabar Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Nijeriya, ya na mai cewa sun kona tutar Amurka ne saboda yadda ta yi gum da bakin ta a kan ci-gaba da tsare Zakzaky.