Home Labaru Bukatar Sulhu: Shekau Ya Maida Wa Gwamna Zulum Martani

Bukatar Sulhu: Shekau Ya Maida Wa Gwamna Zulum Martani

1432
0
Bukatar Sulhu: Shekau Ya Maida Wa Gwamna Zulum Martani
Bukatar Sulhu: Shekau Ya Maida Wa Gwamna Zulum Martani

Rahotanni na cewa, shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi watsi da kiran gwamna Babagana Zulum na jihar Borno na bukatar rungumar sulhu don a samu zaman lafiya.

Yayin da gwamna Zulum ke kira ga mayaka da kwamandojin kungiyar Boko Haram su ajiye makamai a yi sulhu don a samu zaman lafiya, Shekau ya ce yaki ma yanzu su ka fara.

Wani dan jarida ne mai kusanci da kungiyar Boko Haram Ahmad Salkida, ya fara wallafa martanin Shekau a ranar Lahadi a cikin wasu gajerun sakonni da ya fitar a shafin sa na Tuwita.

A cewar Salkida, Shekau ya yi watsi da tayin da Zulum ya yi masu, duk da yin hakan tamkar wata gata ce da maslaha da gwamnan ya bijiro da su.

Da ya ke magana a kan mayakan kungiyar da kan iya ajiye makaman su, Shekau ya ce ya kamata su sani cewa, wannan aiki ne na Allah ba aikin wani mutum ba.