Home Labaru Zaben Kogi: Dan Marigayi Gwamna Abubakar Audu Ya Maka Oshiomhole Kotu

Zaben Kogi: Dan Marigayi Gwamna Abubakar Audu Ya Maka Oshiomhole Kotu

390
0

Daya daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Kogi na jam’iyyar APC Mona Audu, ya maka jam’iyyar APC da Shugaban ta na kasa Kwamred Adams Oshiomhole kotu.

Mona Audu, ydn takarar kujerar gwamnan jihar Kogi

Audu,wanda ya shigar da karar a babbar kotu da ke Lokoja, ya kuma shigar da kara a kan shugaban kwamitin tantance ‘yan takarar a zaben fidda gwani Sanata Hope Uzodinma da hukumar zabe ta kasa.

A cikin karar,  Auduyayi ikirarin cewa, ya cika duk wasu sharuda da ake neman mutum ya cika domin shiga zaben fidda gwani.

Yace ba tare da bin dokokin da aka tsara na tantance ‘yan takaraba, kwamitin jam’iyyar APC na kasa ya soke sunan shi daga jerin sunayen wadanda aka tantance, inda ya na mai cewa wannan ba al’adar jam’iyyar APC bace,don haka an tauye hakkinsa a matsayin dan takarar gwamna.

Audu ya roki kotu ta bayyana cewa, soke sunan shi daga jerin ‘yan takaraya kasance keta hakkin dan takara kuma matakin ya sabawa kundin tsarin mulkin Nijeriya. 7us