Home Labaru Kiwon Lafiya Corona: Buhari Ya Jinjinawa Dangote Bisa Gudunmuwar Naira Miliyan 200 Da...

Corona: Buhari Ya Jinjinawa Dangote Bisa Gudunmuwar Naira Miliyan 200 Da Ya Bada

996
0
Corona: Buhari Ya Jinjinawa Dangote Bisa Gudunmuwar Naira Miliyan 200 Da Ya Bada
Corona: Buhari Ya Jinjinawa Dangote Bisa Gudunmuwar Naira Miliyan 200 Da Ya Bada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa gidauniyar Aliko Dangote a kan gudunwar kudade da ta yi alkawarin ba gwamnatin tarayya domin dakile yaduwar cutar Corona a Nijeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana haka a ranar Larabar da ta gabata, sannan ya bayyana yadda ya kamata ‘yan Nijeriya su yi idan kasa na fuskantar kalubalan wata annoba.

Adesina ya ce, shugaban kasa Buhari ya jinjinawa gidauniyar Dangote bisa gudunmuwar Naira miliyan 200 da ta bada domin yaki da cutar Corona, tare da yin waiwaye a kan irin gudanmawar naira biliyan daya da gidauniyar ta bada wajen yaki da cutar Ebola a baya.

Shugabar gidauniyar Zuwaira ta ce, taimakon na daya daga cikin manufofin gidauniyar na taimakawa asibitoci da wajen gwaje-gwaje, domin kula da kawar da cutar a hanyoyin shigowa Nijeriya, lamarin da zai bada dama wajen tabbatar lafiya kasa baki daya.