Home Home Kisan Gilla: Dalibi Ya Soka Wa Abokin Karatunsa Wuka Har Lahira a...

Kisan Gilla: Dalibi Ya Soka Wa Abokin Karatunsa Wuka Har Lahira a Bauchi

157
0

Wani matashi mai shekaru 22 da ke ajin karshe a Kwalejin Ilimi ta Adamu Tafawa Balewa ya soka wa wani abokin karatunsa mai suna Usman Umar wuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce tuni wanda ake zargin ya shiga hannu.


 Ya kara da cewar a ranar Litinin 28-11-2022 ne da karfe 1:00 na rana jami’an rundunar ta Yan sanda suka samu labarin wani dalibi da ke ajin karshe a Kwalejin Ilimi ta Tafawa Balewa ya soki abokin karatunsa mai suna Usman Umar mai shekaru 25 da wuka a ciki.


Bincike ya bayyana cewar Rigima ta barke tsakaninsu ne bayan margayin ya tuhumi wanda ake zargi da tafiya wani wuri ba tare da ya sanar da shi ba.


Daga nan dambe ya kaure tsakaninsu sai wanda ake zargin ya ciro wuka daga aljihunsa ya soka masa a ciki inda Allah yay i masa cikawa a asibiti.

Leave a Reply