Home Home Ta’addanci: Kasurgumin Dan Bindiga Ya Shiga Hannu Bayan Shekara 7 Ana Farautarsa

Ta’addanci: Kasurgumin Dan Bindiga Ya Shiga Hannu Bayan Shekara 7 Ana Farautarsa

181
0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra ta tabbatar da cafke wani mutum mai suna Matthew Nwankwo, wanda ake zargin shugaban wata kungiyar masu garkuwa da mutane ne, shekara bakwai bayan ayyana ana nemansa ruwa a jallo.

Tun a 2015 ne Nwankwo ya tsere lokacin da gwamnatin Anambra ta rushe gidansa da ke kauyen Umuobindo a garin Nteje na Karamar Hukumar Oyi bayan da aka gano yana amfani da gidan a matsayin maboyar mutanen da suka yi garkuwa da su.
 ‘Yan sanda sun kama wanda ake zargin bayan da jami’an tsaro suka samu bayanan sirri kan maboyarsa.


DSP Tochukwu Ikenga, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da damke wanda ake zargin, a cewar kakakin, kasurgumin dan bindigar da yaransa sun addabi jihar da kewayenta wajen fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Leave a Reply