Home Labaru Siyasar 2023: Yadda Ikpeazu Ke Son Kawar Da Abaribe a Majalisa

Siyasar 2023: Yadda Ikpeazu Ke Son Kawar Da Abaribe a Majalisa

99
0

Bisa ga dukkan alamu za a yi dauki ba dadi kan kujerar Sanatan Abia ta Kudu a Zaben 2023 tsakanin gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu na Jam’iyyar PDP da Sanata mai ci, Eyinnaya Abaribe na APGA.

Tun a matakin yakin neman zabe, kafin a je akwatin zabe masu lura da harkokin siyasar jihar na hasashen kusan kunnen doki ’yan takarar za su yi a zaben da ke tafe.
Abaribe sanannen dan Majalisar Dattawa ne da ya shekara 16 a jere yana wakiltar Abia ta Kudu.


Kafin sauya shekarsa daga PDP zuwa APGA, ya kasance Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, inda a matsayinsa na jagoran ’yan adawa a majalisar ya rika caccakar Gwamnatin Jam’iyyar APC har ya taba neman Shugaba Buhari ya yi murabus kan karuwar matsalar tsaro a Najeriya.


Caccakar da yake wa gwamnati da tsayawarsa kai da fata kan wasu abubuwan da suka shafi kasa sun kara masa farin jini a wurin jama’ar Abia ta Kudu da uwar Jam’iyyar PDP da ta jihar da ma yankin Kudu maso Gabas baki daya.


Farin jininsa a yankin ya kara karuwa bayan ya yi ta kiraye-kirayen neman a saki Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda gwamnati ke tsare da shi — sannan ya tsaya a matsayin mai karbar belinsa.

Leave a Reply