Home Labaru Kisan Gilla: An Gano Karin Manoma Da Mayakan Boko Haram Su Ka...

Kisan Gilla: An Gano Karin Manoma Da Mayakan Boko Haram Su Ka Kashe A Jihar Borno

364
0

Gwamnatin jihar Borno, ta ce adadin manoman da mayakan
Boko Haram su ka kashe a baya-bayan nan su na karuwa,
sakamakon ci-gaba da gudanar da bincike da ake yi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Baba Kura Abbajato, ya ce a
halin yanzu adadin manoman da aka gano mayakan Boko
Haram sun yi wa kisan gilla ya kai 81.

Baba Kura ya kara da cewa, akalla mutane 111 ne ke gonar
yayin da kungiyar ta Boko Haram ta kai masu mummunan
farmakin.

Kafin sanarwar da gwamnatin jihar Borno ta fitar a baya-bayan
nan, an yi ta samun rahotanni masu cin karo da juna dangane da
adadin manoman da su ka rasa rayukan su a harin, inda da farko
gwamnatin tarayya ta ce mutane 43 ne, yayin da majalisar
dinkin duniya ta ce adadin ya kai 110.

Tuni dai shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya
tabbatar da cewa, mayakan sa ne su ka kashe manoman shinkafa
78 a Kwashabe da ke Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno.