Gwamnatin Najeriya ta kulla wata yarjejeniyar fahimtar juna da
Hukumar Dake Kula da Sojojin Kasar Sin wato China kan yaki
da ‘yan ta’adda.
Hakan ya biyo bayan sanya hannu kan kulla wata alaka da
kasashen biyu suka yi a Shelkwatar Tsaro ta Kasa dake Abuja,
sakamakon bukatar da Najeriya ta yi na neman taimakon agajin
Sojoji daga kasar ta China.
Ministan Tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi,
mai ritaya, da Mukaddashin Jakadan Kasar China a Najeriya,
Mr. Zhao Yong, ne suka rattaba hannun a madadin kasashen
biyu.
Magashi, ya ce babu tantama idan Najeriya ta sami taimakon
sojoji daga kasar China zai taimaka mata wurin kawo karshen
ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa, ya ji dadi da aka fahimci cewa
matsalar tsaro da ta’addanci matsala ce da ta addabi duniya ba
iya Najeriya kadai ba, dan haka ya ce akwai bukatar a hada kan
dukkan kasashe wuri guda don yakar ayyukan ta’addanci.
You must log in to post a comment.