Home Labaru Boko Haram: Gwamnonin Arewa Sun Goyi Bayan Gayyato Sojojin Haya

Boko Haram: Gwamnonin Arewa Sun Goyi Bayan Gayyato Sojojin Haya

223
0

Gwamnonin jihohin arewa maso gabashin Nijeriya, sun goyi
bayan kiraye-kirayen da ake yi wa gwamnatin tarayya na dauko
sojojin haya domin murkushe mayakan Boko Haram da su ka
addabi yankin.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya bayyana matsayin
gwamnonin, yayin da su ka ziyarci gwamna Zulum na jihar
Borno, domin jajenta ma shi a kan kisan gillar da mayakan Boko
Haram su ka yi wa manoma a karamar hukumar Jere.

Gwamnonin sun ce, dari bisa dari sun goyi bayan jerin bukatu
ko shawarwarin da gwamnan Borno ya mika wa gwamnatin
tarayya a kan murkushe kungiyar Boko Haram, wanda cikin su
har da bukatar dauko sojojin haya.

Baya ga gayyato sojojin haya, gwamnan Borno ya kuma bukaci
daukar karin dubban matasa aikin soja, musamman daga cikin
‘yan Civilian JTF da suka shafe shekaru su na taimaka wa
dakarun Nijeriya wajen yakar Boko Haram.

Sauran bukatun da gwamnan ya mika kuma sun hada da sayen
motocin yaki masu sulke, da isassun makaman da za su taimaka
wa sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen samun
nasarar murkushe kungiyar Boko Haram.