Home Labaru Tsaro Kisan Gilla: Ƙungiyoyin Arewa Na Neman A Hukunta Waɗanda Suka Kashe Musulmai...

Kisan Gilla: Ƙungiyoyin Arewa Na Neman A Hukunta Waɗanda Suka Kashe Musulmai A Filato

91
0
Miyetti-Allah

Ƙungiyoyin fararen-hula na ci gaba da yin Allah-wadai da kisan-gillar da aka yi wa wasu matafiya Musulmi a jihar Filaton a ranar Asabar din da ta wuce.

Kazalika kungiyoyin sun yi zargin cewa rashin zartar da hukunci ne ke sa ya wasu mutane yin irin wannan aika-aikar.

Kimanin mutum talatin ne suka mutu sakamakon wani hari da ake zargin `yan kabilar Irigwe da kaiwa kan motar matafiyan a cikin birnin Jos, amma sun musanta wannan zargi.

Kungiyoyin fararen-hular, sun nuna takaici da kuma alhini game da kisan-gillar da aka yi wa matafiya Musulmin a gada-biyu da ke titin Rukuba a cikin birnin Jos…kisan da hatta mahukunta na zargin `yan kabilar Irigwe da aikatawa, duk kuwa da cewa shugabanninsu sun fito sun musanta.