Home Labaru Kisan Jos: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bukaci A Biya Diyya

Kisan Jos: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bukaci A Biya Diyya

61
0
Sheikh Dahiru Bauchi

Babban shehin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta biya diyyar mabiyan sa da aka karkashe a yankin Gada-Biyu na garin Jos na Jihar Filato a ranar Asabar.

Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya bukaci biyan diyyar daga Gwamnatin Jihar Filato ya kuma nemi a hukunta wadanda suka kashe almajiran nasa guda 30 tare da jikkata wasu da dama.

Shehin malamin, wanda Shugaban Kasa ya yi wa ta’aziyya bisa wakilcin Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami, ya bayyana bukatar biyan diyya ga iyalan mamatan da kuma hukunta masu laifin ne a wata zantawa da Sashen Hausa na BBC ya yi da shi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma gargadi al’ummar Musulmi da su nisanci daukar doka a hannunsu da sunan daukar fansa a kan kisan matafiyan da aka yi.

Tun bayan faruwar lamarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a kamo tare da hukunta wadanda suka yi wa matafiyan kisan gilla.