Home Labaru Ilimi Yawan Al’Umma: Obasanjo Ya Ce Karuwar ‘Yan Nijeriya Na Tayar Masa Da...

Yawan Al’Umma: Obasanjo Ya Ce Karuwar ‘Yan Nijeriya Na Tayar Masa Da Hankali

56
0
Obasanjo

 

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa hauhawar adadin al’ummar Nijeriya na matukar tayar mishi da hankali musamman in ya yi la’akari da halin da kasa take ciki, a cewar shi nan gaba ciyar da al’ummar zai zama abu mai mugun wahala ga mahukunta.

Yace Duk lokacin da ya tuna da yawan al’ummar da ake da ita a kasar mu, sai ya kasa rintsawa, kan tunanin ta wacce hanya zamu ciyar da su? Domin Kwanakin baya alkaluman hasashe suka bayyana yadda nahiyar Afirka za ta fada cikin matsalar karancin abinci.

Obasanjo ya ci gaba da cewa; rashin aikin da matasan Afirka suke fama da shi, yafi na kusan dukkan sassan duniya, Dole kasashen Afrika su samar da hanyar da zasu magance wannan matsalar tun kafin ta tumbatsa ta addabi kowa.

Yace Dole ne hukumomin Afirka su maida hankali kan ilmantar da ‘yan baya, Saboda kowa ya san yadda ilimi yake taimakawa kasa wajen magance matsalolinta irinsu rashin aikin yi, talauci da ma uwa-uba rashin tsaro.