Rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya Abuja, ta kara kaimin gudanar da sintiri a birnin domin tabbatar da ganin an yi bukukuwan Kirsimati lami lafiya.
Kwamishinan ‘yan sanda na birnin Mista Bala Ciroma ya bayyana haka, a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja.
Bala Ciroma ya ce, rundunar ta ninka yawan jami’an ta da za su tattara bayanan sirri da kuma duba ababen hawa a kan tituna.
Kwamishinan
ya jaddada cewa, ayyukan su na kakkabe masu garkuwa da mutane daga birnin su na
nan su na ci-gaba da yi, sannan ya yi kira ga mazauna birnin su yi taka-tsantsan
wajen daukar ‘yan aikin cikin gida da direbobi da kuma masu gadi.