Home Labaru Dubu Ta Cika: ‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Su Ka Yi Garkuwa...

Dubu Ta Cika: ‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Su Ka Yi Garkuwa Da Dan Majalisa

725
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta ce ‘yan sandan Puff-Adder sun kama ‘yan bindigar da su ka yi garkuwa da dan majalisar dokoki ta jihar Kaduna Sulaiman Dabo, da daliban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar Yakubu Sabo ya sanya wa hannu, ya ce tun bayan sakin wadanda aka yi garkuwa da su, jami’an ‘yan sanda na ‘Operation Puff-Adder su ka fantsama cikin dazuzzukan da ke kewaye da Kangimi domin kama masu garkuwa da mutanen.

Ya ce ‘yan sanda sun dira wuraren boyon maharan da ke Maigiginya da Gurguzu duk a karamar hukumar Igabi, inda su ka kama wasu masu garkuwa da mutane sannan su ka kashe wasu tare da kwato bindigogi kirar AK47.

Haka kuma, wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da aka kama Buhari Bello, ya ce kungiyar su ya hada da masu garkuwar da ke aika-aika a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, ya bukaci mutane su cigaba da taimaka wa ‘yan sanda da bayannan da za su sa a bankado maboyar wadannan ‘yan ta’adda.

Leave a Reply