Home Labaru Ta’aziyya: Shugaba Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Robert Mugabe

Ta’aziyya: Shugaba Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Robert Mugabe

219
0
Robert Mugabe, Mai Rasuwa Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe
Robert Mugabe, Mai Rasuwa Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi alhinin mutuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, wanda ya mutu ya na da shekaru 95 a duniya.

Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Mugabe ne ta bakin kakakin sa Femi Adesina, inda ya taya iyalai da ‘yan’uwa da abokan arzikin sa jimamin rashin da su ka yi.

Shugaba Buhari, ya ce Mugabe ne ya jagoranci yakin neman ‘yancin kasar Zimbabwe daga mulkin mallaka na turawan yamma.

Ya ce tarihi ba zai manta da sadaukarwar da Mugabe ya yi wa al’ummar sa ba, musamman gwagwarmayar da ya yi don ceto jama’ar sa daga takunkumin tattalin arziki da kuma siyasa.

Robert Mugabe dai ya rasu ne a wani babban asibitin kasar Singapore, bayan ya kwashe tsawon lokaci ya na jinya, sai dai gwamnatin kasar Zimbabwe ba ta bayyana irin cutar da ke damun shi ba.

Marigayin ya kwashe tsawon shekaru 37 ya na mulkin kasar Zimbabwe, tun bayan samun ‘yancin kasar daga hannun turawa a shekara ta 1980, har sai a watan Nuwamba na shekara ta 2017 ne Sojoji su ka hambarar da gwamnatin sa.