Home Labaru Kididdiga: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Shugabannin Hukumar NBS

Kididdiga: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Shugabannin Hukumar NBS

298
0

Majalisar dattawa ta amince da nadin mukaman shugaba Muhammadu Buhari a hukumar kididdiga ta kasa.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, Majalisar ta amince da kudirin shugaba Buhari, biyo bayan samun rahoton sakamakon binciken da kwamitin tsare-tsaren kasa da kuma tattalin arziki na majalisar ya gabatar.

Majalisar dai ta amince da Kabiru Nakaura a matsayin shugaban hukumar kididdiga ta kasa mai reshen Arewa maso Yamma.

Sauran shugabannin hukumar kuma sun hada da Akinola Bashir daga Kudu maso Yamma, da Moses Momoh daga Kudu maso Kudu, da Wallijoh Ahijoh daga Arewa ta Tsakiya, da Adam Modu daga Arewa maso Gabas, da kuma Nwafor Chukwudi daga Kudu maso Gabas.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya taya sabbin shugabannin murna, tare da yi masu fatan alheri, ya na mai gargadin su a kan jajircewa wajen yi wa kasar su hidima.pen(“G�鶇�”-

Leave a Reply