Gwamnatin tarayya ta ce, yanzu haka ‘yan Nijeriya 446 ke tsare a gidajen yarin kasar Hadaddiyar Daular Larabwa bisa aikata laifuffukan da ke da nasaba da safarar kwayoyi da wasu laifuffuka.
Yayi da ya yi wa ‘yan Nijeriya mazauna kasar jawabi a gaban shugaba Muhammadu Buhari, Jakadan Nijeriyar a birnin Dubai Ambasada Mohammed Dansanta Rimi, ya ce akwai tarin ‘yan Nijeriya da ke aikata ayyukan assha a kasar.
Kalaman Jakadan kuwa su na zuwa ne, makonni kadan bayan an kam wasu ‘yan Nijeriyar biyar da ake zargi da laifin fashi da makami a Kasar.
Idan dai za a iya tunawa, a cikin watan da ya gabata, an yanke ma wasu ‘yan Nijeriya hukuncin kisa, wasu kuma na daure a gidajen yarin Saudiya bayan samun su da aikata ba daidai ba.