Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty ta ce, shekaru takwas bayan kungiyar Boko Haram ta sace ‘yan matan makarantar Chibok 276, sama da dalibai dubu 1 da 500 wasu kungiyoyi su ka sace.
Amnesty International ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto da ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, inda ta ce a cikin dalibai 276 na Chibok da aka sace, an kashe 16 kuma har yau ba a san inda 109 su ke ba.
Kungiyar ta kara da cewa, an sace dalibai dubu 1 da 500 a cikin watanni 22 ne, kuma har zuwa wannan lokacin akwai dalibai kimanin 120 da ke hannun wadanda su ka sace su.
Daga cikin dalibai 102 da aka sace a makarantar gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri, har yanzu 9 su na hannun ‘yan bindiga, sannan ba a sako daya daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist ta Kaduna da aka sace ba.
You must log in to post a comment.