Home Home Zargin Zamba: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi Da Hukuncin Da Ya...

Zargin Zamba: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi Da Hukuncin Da Ya Wanke Aa Zaura

81
0
Wata Kotun Daukaka Kara da ke Kano, ta yi watsi da hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya na wanke mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar Abdulsalam Sale Abdulkarim Zaura bisa zargin zamba.

Wata Kotun Daukaka Kara da ke Kano, ta yi watsi da hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya na wanke mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar Abdulsalam Sale Abdulkarim Zaura bisa zargin zamba.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da Zaura a gaban Babbar Kotun Tarayya, bisa zarge-zarge biyar da su ka shafi zamba cikin aminci.

EFCC dai ta zargi Zaura da yi ma wani dan kasar Kuwait zambar Dala miliyan daya da dubu dari uku da ashirin, bayan ya yi ikirarin cewa ya na harkar kasuwancin gidaje a Dubai da Kuwait da wasu kasashen Larabawa.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin ta na Facebook, ta ce ranar 9 ga watan Yuni na shekara ta 2020, Mai Shari’a A. L Allagoa ya wanke Zaura daga dukkan zarge-zargen, sai dai mai shigar da kara Musa Isah ya nemi Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin karamar kotun.