Home Labaru Kididdiga: Al’ummar Duniya Za Su Zarce Fiye Da Biliyan Tara A Shekara...

Kididdiga: Al’ummar Duniya Za Su Zarce Fiye Da Biliyan Tara A Shekara Ta 2050 – MDD

352
0

Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa, yawan mutanen duniya zai karu zuwa biliyan 9 da miliyan 700 nan da shekara ta 2050,  sabanin biliyan 7 da doriya da ake da su yanzu.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa, nan da shekara ta 2,100 yawan mutane zai kai biliyan 11, kasancewar kasar Sin da ake cewa tafi kowacce kasa yawan al’umma, kuma za ta samu raguwar mutane sosai nan da shekara ta 2050.

Majalisar dinkin duniya ta ce, kasashe 9 aka gano za su fuskanci karuwar mutane sosai bisa hasashen sun hada da, Indiya da Nijeriya, Pakistan da Jamhuriyar Congo da Habasha da Tanzania da Indonesia da Masar da kuma Amurka.

Leave a Reply