Home Labaru Bayan Zabe 2019: INEC Za Ta Dauki Masu Yi Wa Kasa Hidima...

Bayan Zabe 2019: INEC Za Ta Dauki Masu Yi Wa Kasa Hidima Da Su Ka Nuna Kwazo A Aikin Su

393
0
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta kasa, INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za ta dauki masu yi wa kasa hidima da suka jajirce a lokacin gudanar da aikin zaben shekara ta 2019 aiki.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a Abuja, a lokacin da ake bada kyautar wayoyin salula da kwamfutocin da jami’an sa ido a zaben 2019 na gamayyar kasashen turai su ka yi amfani da su.

Yakubu ya ce, an samu damar gudanar da zaben ne saboda gudummuwar da masu yi wa ksa hidima su ka bada a matsayin jami’an hukumar na wucen gadi.

Shugaban wakilan kungiyar gamayyar kasashen turai na Nijeriya, Ambasada Ketil karlsen, ya bayyana matasan a matsayin ginshikin dimukaradiyya, saboda su ne mabudin gyara gudanar da zabe a Nijeriya.

Ya kara da cewa kungiyar tarayyar Turai ta gabatar da bincike game da zaben Nijeriya na shekara ta2019, kuma binciken ya nuna cewa, , duk da zaben a kwai kurakure  alamu sun tabbatar  da cewa an samu ci-gaba.

Babban daraktan hukumar masu yiwa kasa hidima NYSC Burgediya janaral Shuaibu Ibrahim, ya ce fiye da matasa 300,000 ake dauka a cikin tsarin yiwa ksa hidima  duk shekara, kuma ana koyar da su abubuwa da dama ta yadda za su dogara da kan su don cigaban kan su da ma kasa baki daya.

Leave a Reply