Home Labaru Diplomasiyya: Macron Ya Bukaci Iran Ta Kara Hakuri A Kan Yarjejeniyar Nukiliya

Diplomasiyya: Macron Ya Bukaci Iran Ta Kara Hakuri A Kan Yarjejeniyar Nukiliya

493
0
Emmanuel Macron, Shugaban Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel ya bukaci Iran ta kara hakuri tare da nuna halin dattaku, bayan ta ce za ta ninka aikin samarwa, tare da tace makamashin nukiliyar ta da take tarawa har sai ta zarce iyakar da aka mata, a yarjejeniyar da ta kulla da manyan kasashen Turai a shekara ta 2015.

Sanarwar yin watsi da yarjejeniyar nukiliya da Iran ta bayar, ta zafafa matsin lamba kan batun, tun bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar a shekarar da ta gabata.

Shugaba Macron ya ce, idan rikicin yankin gabas ta Tsakiya ya munana, ba zai tsinana wa kowa komai ba, saboda haka zai ba Iran da sauran kasashen duniya shawara a kan su janye daga wannan matakin, domin zai bata rawar su da tsalle.

Amurka ta zargi Iran da kai hari kan wasu tankokin mai a tekun Oman, a makon da ya gabata, zargin da Iran ta ce ba shi da tushe ballantana makama.

Shugaban Faransa dai, ya yi kaffa- kaffa wajen yin tsokaci game da wannan batu, yana mai cewa dole sai an kammala tattara bayanai game da harin da aka kai wa tankokin mai a teku kafin a ayyana wani a matsayin mai laifi.Ya kara da cewa, wannan yanayi da ake ciki yana bukatar a yi sara ana duban bakin gatari, saboda a kasance a natse.

Leave a Reply