Home Labaru Kenya: An Sace Makaman ‘Yan Sanda Da Ke Kallon Wasan Kwallo

Kenya: An Sace Makaman ‘Yan Sanda Da Ke Kallon Wasan Kwallo

249
0

Wasu  barayi sun fasa ofishin ‘yan sandan Kenya, inda suka sace makamai a daidai lokacin da jami’an ‘yan sandan ke kallon wasan Barcelona da Manchester United a gasar zakarun Turai a ranar Talata a wani gidan kallo.

Jaridun Kenya sun rawaito cewa, barayin sun sace manyan bindigogi uku da kuma jigidar alburusai na ‘yan sandan Kobujoi dake lardin Nandi a kasar.

Bayan ‘yan sandan sun dawo daga gidan kallon ne suka tarar an fasa dakin ajiyar makamansu.

Rahotanni na cewa, ana ci gaba da bincike da kuma farautar barayin da suka sace makaman.

Tuni wannan al’amari ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta a kasar, inda wasu ke zargin ‘yan sandan da yin sakaci da aikinsu na kare lafiya da dukiyar al’umma duk da kudin albashi da ake biyan su domin wannan aiki.