Home Labaru Kamaru: Za A Maido Da ‘Yan Najeriya Dubu 4 Gida

Kamaru: Za A Maido Da ‘Yan Najeriya Dubu 4 Gida

232
0

Hukumomin Kamaru sun bayyana cewar sun shirya tsaf domin mayar da ‘yan Najeriya dubu 4 dake gudun hijira a sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.

Gwamnan Lardin Arewa mai nisa, Mijinyawa Ciroma Bakari, ya bayyana cewar daga ranar 29 ga watan nan, za su fara mayar da ‘yan gudun hijirar dake sansanin Minawao, wadanda suka bayyana aniyar su ta komawa gida domn zabin kansu.

Bakari, ya ce sun tattauna da hukumomin Najeriya kuma sun amince da shirin mayar da ‘yan gudun hijirar da suka fito daga Jihar Adamawa.

Rahotanni sun ce, shirin mayar da ‘yan gudun hijirar bai shafi wadanda suka fito daga Jihar Borno ba, saboda rashin kwanciyar hankali a yankunansu.Majalisar Dinkin Duniya ta ce, sansanin Minawao ya karbi baki ‘yan gudun hijira 57,000 daga Najeriya

Leave a Reply