Home Labaru Sufuri: Kungiyar Eu Za Ta Lafta Wa Amurka Harajin Dala Biliyan 12

Sufuri: Kungiyar Eu Za Ta Lafta Wa Amurka Harajin Dala Biliyan 12

211
0

Kungiyar tarayyar turai na shirin lafta wa Amurka harajin da ya kai Dala biliyan 12 a matsayin martani kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na bayar da tallafi ga kamfanin jiragen sama na Boeing abinda ya saba wa dokokin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya.

Daga cikin kayayyakin Amurka da kungiyar tarayyar turai ta ce, za ta lafta wa harajin har da ruwan zuma da safayen motoci da Amurkan ke shigar da su nahiyar Turai, matakin da ka iya farfado da yakin kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.

Kwamishiniyar Kasuwancin Tarayyar Turai, Cecilia Malmstrom ta ce, dole ne kamfanonin kasashen Turai a dama da su a fagen gogayyar kasuwanci cikin adalci, tana mai cewa, wajibi ne su kare masana’antunsu.

Harajin na Dala biliyan 12 da EU ke fatan lafta wa Amurka na zuwa ne bayan ita ma Amurka ta yi barazanar lafta wa Turai harajin Dala biliyan 11 saboda tallafin da ita ma ta bai wa kamfanin jiragen sama na Airbus.

Sai dai Cibiyar Kasuwanci ta Duniya ce za ta kayyade adadin harajin da kowanne bangare zai lafata wa dan uwansa, kuma ana ganin ko kadan harajin ba zai kai yawan kudin da bangarorin biyu ke ambata ba.

Leave a Reply