Shugaba majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce babu wasu kudin kirki da ‘yan majalisar tarayya ke samu kamar yadda ake yadawa.
Sanatan ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin wata kungiyar a ofishin sa da ke Abuja, inda ya ce Kwata-kwata albashin sa da na takwarororin sa bai wuce Naira dubu 750 ba.
Ya ce ‘yan majalisar dattawa da ta wakilai su na karbar albashin su, yayin da shi kan sa ya ke karbar Naira dubu 750 matsayin albashi. Sanatan ya cigaba da cewa, ya yi alkawarin babu wani abin da za a boye wa ‘yan Nijeriya game da ayyukan majalisa musamman bangaren kudi.