Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da zargin da ake yi wa tsohon gwamna Ibikunle Amosun na shigo da tarin bindigogi da alburusai Nijeriya ba bisa ka’ida ba.
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu, ya ce binciken farko da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohamed Adamu ya gudanar, ya nuna cewa babu wani mugun nufi a matakin da Amosun ya dauka.

Garba Shehu, ya ce shugaban ‘yan sandan ya gudanar da binciken farko kuma zai gabatar da jawabi a kan lamarin bindigogin a jihar Ogun.
Idan dai za a iya tunawa, rahotanni sun ce a baya tsohon gwamnan ya maida tarin makamai da alburusai da ya ajiye a gidan gwamnati. Sai dai a na shi bangaren, Amosun ya karyata zancen mika bindigoi AK47 guda 1000 ga kwamishinan ‘yan sanda Makama, kwana daya kafin ya bar kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2019.
You must log in to post a comment.