Home Labaru Nadin Ministoci: Jam’iyyar PDP Ta Ja Hankalin Shugaba Muhammadu Buhari

Nadin Ministoci: Jam’iyyar PDP Ta Ja Hankalin Shugaba Muhammadu Buhari

466
0

Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaba Muhammdu Buhari ya yi gaugawar nada ministocin sa, inda ta yi gargadi cewa rashin nada ministocin a kan lokaci na iya jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arziki.

PDP, ta kuma yi kira ga shugaba Buhari cewa kada ya sake jefa kasar nan a cikin matsin tattalin arziki ta hanyar nuna ya san komai.

Shugaban jam’iyyar na kasa Prince Uche Secondus ya bayyana wa manema labarai cwa, abin takaici ne a ce shugaba Buhari har yanzu bai fitar da sunayen wadanda zai nada a matsayin ministoci bayan watanni uku da cin zabe ba. Secondus, ya ce jinkirin da aka samu wajen nada ministoci a shekara ta 2015 ne ya jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arziki, ta na mai yin kira ga masu zurfin tunani su ja hankalin shugaba Buhari saboda Nijeriya na gab da nutsewa a karkashin mulkin shi.

Leave a Reply