Home Labaru Kaduna: An rage tsawon lokacin fita

Kaduna: An rage tsawon lokacin fita

364
0

An rage tsawon lokacin fitar mutane zuwa sa’a 10 a ranakun Talata da Laraba a Jihar Kaduna.

Daga yanzu sassaucin dokar hana fitar za ta fara aiki ne daga karfe 8 na safiya zuwa 6 na yamma a ranakun Talata da Laraba.

Gwamnatin jihar ta ce masu kayan abinci da magunguna ne kadai aka amince su bude shaguna a ranakun biyu.

Gwamnatin ta kuma haramta ayyukan dukkan nau’ukan baburan haya a fadin jihar, tare da takaita yawan fasinjojin da motocin haya za su dauka zuwa mutum biyu a kowane layi.

Ta kuma wajabta wa masu shaguna da masu sayayya nisantar cinkoso tare da kula da matakan kariya domin kauce wa yaduwar cutar coronavirus

Wannan mataki wani gyaran fuska ne ga sassaucin da da gwamnatin jihar ta fara yi na sa’a 36 a ranakun Talata da Laraba domin ba wa jama’a damar yin cefane da sayen muhimman kayayyakin bukata.

Kakakin Gwamnatin Jihar Kaduna, Samuel Aruuwan, ya ce rage tsawon lokacin fitar ya biyo bayan shawarwarin Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus a jihar ne, domin rage hadarin yaduwar cutar.

A baya Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Hadiza Balarabe Sabuwa, wadda kuma take jagorantar Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus a jihar yi kurarin janye sassaucin dokar sakamakon yadda mutane ke karya dokar hana fitar ta sa’a 24 da aka anya domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Mataimakiyar Gwamnan ta bayyana bacin rai tare da umurtar jami’an tsaro da su dauki mataki a kan masu karya dokar hana fitar.

Sauran matakan da gwamnatin jihar ta dauka sun hada da rufe iyakokinta da makwabtanta, tare da barazanar killace duk wanda ya shigo daga wata jiha na tsawon mako biyu kafin a bari ya shiga cikin jama’a.