Home Labaru Katsina: ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 40

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 40

306
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta  kama ‘yan ta’adda 40 wadanda suka hada da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da ‘yan fashi da makami da matsafa.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Sanusi Buba, ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce an sami nasarar ce bayan shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar ya kaddamar wata runduna mai suna Operation Puff Adder.

Ya ce rundunar za ta bunkasa sintiri damin samun bayanan sirri daga  al’ummar gari da sauran hukumomi ta hanyar atisayen Operation Puff Adder.

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda aka kama  na dauke  da bindiga  kirar AK 47 da man fetir da Babura da adduna da kudi naira milliyan 218.

Kwamishinan, ya ce an kama ‘yan ta’addan ne a lokacin da suka yi garkuwa da wata mata mai suna Hajiya Habiba mai shekara 65 a kauyen yar-Liyau da ke karamar hukumar Kurfi, inda suka bukaci naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.