Home Labaru Iftila’i: Mutun 8 Sun Mutu A Wani Hadari A Jos-Hukumar FRSC

Iftila’i: Mutun 8 Sun Mutu A Wani Hadari A Jos-Hukumar FRSC

175
0

Hukumar kare aukuwar hadurra ta Najeriya a jihar Filato ta mutane 8 sun rasa rayukansu, wasu 148 kuma suka sami rauni sakamakon hadurra 49 da suka auku a tsakanin watan Janairu da Maris na wannan shekerar.

Jami’in ilimantar da jama’a, na hukumar Andrew Bala, ya bayyana haka ga manema labarai a Jos, ya ce akasarin hadurran sun auku ne sanadiyyar gudun ganganci da matsalar burki da kuma lalacewar taya.

Bala, ya ce a watan Janairu an sami hadurra 13, amma babu wanda ya mutu, sai dai mutane 32 sun sami rauni, sannan kuma a watan Maris an sami  hadurra 20, mutum biyar suka mutu inda kuma mutane 84 suka samu rauni.

Bala, ya ce hukumar ta sami nasarar kama ababen hawa dubu 3, da dari 522 sakamakon aikata laifuffuka daban-daban, inda ya yi kira  ga masu ababen hawa musamman masu haya  su rika bin dokokin hanya domin kare  rayuka da dukiyar alumma.