Shugaban rundunar Sojojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce rundunar sojoji za ta dauki mataki na kashin kanta akan wadanda suka taimaka wajen kashe ‘Yan Sanda a jihar Taraba.

Buratai, ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin rundunar ke gudanar da wani taro na tsakiya da kuma na karshen shekara a Abuja.
Ya ce, rundunar ta kammala gudanar da bincikenta domin yanayin kisan yana bukatar gudanar da bincike na musamman daga kowani bangare na hukumomin tsaro.
Ya kuma kalubalanci Kwamandan shiyyar ya sake wayar da kan sojojin da ke yankin akan yadda za su rika hulda da fareren hulda da sauran hukumomin tsaro, saboda lamarin da ya auku ya haifar da mummunan zato da ake yiwa sojojin Najeriya.
Ya kara da cewa ansan sojojin Najeriya da da’a da kuma kwarewa wajen gudanar da ayyukan su da sauran hukumomin gwamnati da sauran al’umma.
Ya ce a matsayin
rundunar sojojin Najeriya ta daya daga cikin hukumomin tsaro, bukatar ta shi ne
marawa sauran hukumomin tsaro da ‘Yan Sanda baya wajen ganin an magance duk
wata barazanar tsaro a kasa.
You must log in to post a comment.