Home Labaru Harin Afirka Ta Kudu: ‘Yan Najeriya Sun Fara Ramuwar Gayya

Harin Afirka Ta Kudu: ‘Yan Najeriya Sun Fara Ramuwar Gayya

767
0

Sakamakon yadda aka kai wa ‘yan Najeriya  hari a kasar Afirka ta Kudu, wasu fusatattun matasa a jihar Legas sun farma wani kamfani mallakar kasar Afrika ta kudu mai suna Shoprite da ke garin Lekki a jihar.

Hakan ya biyo bayan wani sabon hari da aka kai wa ‘yan Najeriya a kasar, inda aka kona musu shaguna da wuraren kasuwanci.

Gwamnatin tarayya ta hannun Ministan harkoikin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya yi Allah wadai da harin kyamar baki da ake kaiwa ‘yan Najeriya a kasar ta Afrika ta kudu, inda ta bayyana a matsayin ayyukan ta’addanci.