Home Labaru Cika Alkawari: Sarkin Bauchi Ya Ja Hankalin ‘Yan Siyasa

Cika Alkawari: Sarkin Bauchi Ya Ja Hankalin ‘Yan Siyasa

594
0

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, ya bukaci zababbun ‘yan siyasa da su yi kokarin cika alkawuran da su ka daukar wa masu zabe a lokacin da su ke yakin neman zabe musamman ta fuskar samar mu su da ababen more rayuwa.

Sarkin Bauchin, wanda shi ne shugaban Jama’atu Nasril Islam reshen jihar Bauchi, ya ce akwai bukatar wadanda aka zaba a kujeru daban-daban su gudanar da aiyukan da jama’ar da su ka zabe su suke tsammani daga gare su.

Ya ce ta hanyar kyautata shugabanci ne kasa za ta samu habaka da ci gaba mai dorewa dan haka ya zama wajibi shugabanni su sauke nauyin da ke wuyar su.

Sarkin ya ce daga cikin abinda al’umma suke bukata a kwai magance matsalolin yaduwar cututtuka ta hanyar samar da ruwa mai tsafta da kuma tabbatar da tsaftar muhalli.

A cewar sanarwar, ta hanyar kyautata ruwan sha da muhalli za a samu damar shawo kan yaduwar cutuka kamar su kwalera da maleriya hadi da wasu ‘yan cutuka da ke bazuwa gami da illata lafiyar al’umma.

Daga bisani Sarkin ya nemi al’umma da suke sanar da hukumomin da abun ya shafa da zarar sun samu barkewar wata cuta domin shawo kan matsalolin cikin gaggawa.