Home Labaru Kashe Kashe: Al’ummomin Jihar Katsina Sun Fara Kaurace Wa Muhallan Su

Kashe Kashe: Al’ummomin Jihar Katsina Sun Fara Kaurace Wa Muhallan Su

451
0

Sakamakon yawaitar ta’addancin ‘yan bindiga da ke kara jefa rayuwar al’umma cikin mawuyacin hali, jama’ar kauyen Maidabino da ke karamar hukumar Danmusa a jihar katsina sun fara tserewa da nufin neman mafaka a wasu yankuna domin tsira da rayukan su.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani Usman Abdulmuminu Maidabino, ya ce hakan ta faru ne sakamakon harin da ‘yan bindiga su ka kai a da yammacin ranar Larabar da ta gabata.

Yayin da su ka kai harin, ‘yan bindigar sun kashe mutane uku, sannan su ka farfasa shagunan jama’a su ka kwashe kayayyaki.

Rahotanni na cewa, yankin kananan hukumomin Danmusa da Batsari da Kankara sun dade su na fama da matsalar tsaro, musamman harin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.