Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Fara Binciken Sanata Abbo

‘Yan Sanda Sun Fara Binciken Sanata Abbo

543
0
Frank Mba, Mai Magana Da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda
Frank Mba, Mai Magana Da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta fara binciken Sanata Elisha Abbo, bisa zargin ya cin zarafin wata mata a wani kantin saida robobin jima’i a Abuja.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda Frank Mba ya shaida wa manema labarai cewa, shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammed Adamu ya bada umarnin a fara binciken Sanatan.

‘Yan Nijeriya dai na ci-gaba da bayyana ra’ayoyin su, tun bayan da kafar yada labarai ta Premium Times ta wallafa wani bidiyo mai tsawon mintuna 10 da ke ikirarin nuna sanatan ya na dukan wata mata a cikin wani shago. Frank Mba, ya ce ‘yan sanda sun tuntubi matar, kuma za su yi nazari a kan bidiyon kafin a karshe za su sanar da ‘yan Nijeriya abin da binciken ya gano.