Home Labaru Kasafin Kudin 2022: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Sanya Hannu

Kasafin Kudin 2022: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Sanya Hannu

309
0

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya kattaba hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2022 inda ya zama doka.

Kasafin da ya kai na Naira Tiriliyan 17.127 an yi masa laƙabi ne da kasafin habaƙa tattalin arziƙi da tafiyar da shi.

Cikin waɗanda suka halarci sa hannu a kasafin kuɗin har da Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan, da shugaban Majalsar Wakilai Femi Gbajabiamila, da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma Ministar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare Zainab Ahmed.

A shekara ta 2021 mai ƙarewa dai an yi kasafin na Naira Tiriliyan 13.588 ne  inda daga baya aka ƙara biliyan 983 a kai.

Leave a Reply