Home Labaru Isra’Ila Ta Harba Makami Mai Linzami Tashar Jirgin Ruwan Siriya

Isra’Ila Ta Harba Makami Mai Linzami Tashar Jirgin Ruwan Siriya

89
0
An Israeli flag blows in the wind from an elevated view of the Western Wall. Jewish orthodox believers read the Torah and pray facing the Western Wall, also known as Wailing Wall or Kotel in Old City in Jerusalem, Israel. It is small segment of the structure which originally composed the western retaining wall of the Second Jewish Temple atop the hill known as the Temple Mount to Jews and Christians.

Rahotanni daga Siriya na cewa Isra’ila ta kai wani hari ta sama a tashar jiragen ruwan kasar dake yankin Latakia, harin da ke zama na biyu da aka kai tashar a wannan watan.

Rahotanni na nuni da cewa Isra’ilar ta kaddamar da harin ne da makami mai linzami daga tekun Bahar Rum.

Harin dai ya haifar da tashin gobara da kuma lalacewar wasu kayan aiki.

Ko a ranar 7 watan Disambar nan Isra’ilar ta kai hari kan wani jirgin ruwan Iran a Latakia, sai dai kuma ba a sami asarar rayuka ba.

Tun bayan barkewar yakin basasa a Siriya a shekarar 2011 ne Isra’ila ta ke kaddamar da hare-hare ta sama ga makwafciyarta mai fama da rikici, mafi akasari kan dakarun gwamnati da dakarun kawancen Iran da kuma mayakan Hizbullah.