Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta kama wasu ma’aikatan hukumar tara haraji ta kasa, bisa zargin su da hannu a harkallar biliyoyin naira na harajin da ‘yan kasa ke biya.
Daga cikin wadanda aka kama kuwa akwai Babban Daraktan harkokin kudi na hukumar Mohammed Auta, da babban daraktan a hukumar mai suna Peter Hena.
Kakakin hukumar Orilade Tony ya tabbatar wa manema labarai cewa, hukumar EFCC ta yi awon gaba da wadannan mutane, amma da zarar ya samu karin bayani zai sanar wa duniya.